Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Matashi sai Matashi: Kwamared Sani Bala Tela


Kwamared Sani Bala Tela
Kwamared Sani Bala Tela

Kwamred Sani Bala wanda aka fi sani da Sani Tela- yayi kira ga Matasa cewa ya kamata susan yancin su, ya zama wajibi su san cewar matasa su ke da kaso mafi yawa a cikin al'ummar Najeriya wanda shine abinda zai basu hubbasa na tabbatar da cewar matsalar matashi sai matashi ne zai iya magance ta.

Yace 'yan siyasa na anfani da matasa domin su cimma burinsu a matsayin wani mataki da suke dauka don burinsu na cin zabe da zarar an kammala zabe sai su manta da su.

Matasa a yanzu sun taka duk wata rawa ta cigaba, misali a fannin ilimi, wayewar kai, sanin hanyoyin tafiyar kasa, duk matasa a yanzu sun san yadda zasu kawo gyara ga kasa Najeriya, ila babban abinda ke ci masu tuwo a kwarya dai baya wuce rashin kayan aiki da zasu gudanar da harkar zabe.

Akan haka ne a yanzu matasa ke yunkurin hada kan matasa , ta hanyar tabbatar da duk wani da yake da bukatar tsayawa takarar siyasa sai matasa sun tabbatar da cewa dan takara yayi wa alummarsa aiki , ya cancanci kuriar matasa.

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG