Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Da Aka Tarwatsa A Bauchi Zasu Koma Abuja


Biyo bayan tarwatsa wasu matasa da jami’an tsaron suka yi a makon da ya gabata daga sansanin da zasu samu horo a kan aiyukan da suka jibanci kayan sarki a garin Bauchi, fiye da su dubu daya , yanzu haka za’a ci gaba da gudanar da wannan shiri a birnin Abuja.

Wadannan matasa dake halartar wannan horarwa sun fito daga jihohin goma sha tara, na arewacin Najeriya, ne shirin kuma na karkashen kulawar Usman Shuaibu Dass, na “Forum For All Patriotic Members Of APC”.

Mai kula da shirin Usman Shuaibu Dass, ya ce yana tare da jam’iyyar APC, ba kamar yadda wasu ke cewa jam’iyyar APC, bata san dashi ba. Ya furta hakkan ne a hira da wakilin muryar Amurka Abdulwahab Muhammad, dake garin Bauchi.

Daya daga cikin matasan dake halartar wannan horarwa daga jihar Filato, Bashir Ibrahim, ya ce ,mai kula da shirin Shuaibu Dass, ya bukaci shuwagabanin matasan dasu hadu dashi a Abuja, domin a cewarsa sansanin zai koma Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

XS
SM
MD
LG