Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Fara Yunkurowa A Bollywood


Jhanvi Kapoor
Jhanvi Kapoor

Wata matashiya mai shekaru 20, da haihuwa Jhanvi Kapoor, ta fara kama hanyar yin fice a Bollywood, inda ta fara da salon sitiru inda take baiwa marada kunya wajen nuna nata salon sitirun.

Ita dai wannan matashiya ta samin goyon baya da rakiyan yayarta ta mai suna Sridevi da kuma mahaifiyarta, Boney Kapoor, kuma sunan Kapoor dai ba bako bane ya kasance sananen a faggen fina finai a Bollywood.

Salon sitirun wannan matashiya dai yana daukar idon mutane kuma an bi diddigin irin sitirun da take sawa sun kasance daga manya kuma fitattun masu masu sana’ar sitiru take muamala dasu kamar su Karan Johar, Manish Malhotra da dai sauransu wadan suma suna kokaroin ganin cewa duk sitirun daga garesu su mkasance masu haskaka tautaruwar.

Ita dai Jhanvi Kapoor,ta kasance dogowar mace kuma kyakkyawa ma tafiya da kwarjini kuma gashi tayi kama da mahaifiyarta, kusan kowane sitira ta sa kai kace da shi ta zo duniya ganin yadda suke yi tsaf a jikinta.

Bollywood ta kasance tana baiwa matasa dama da kuma goyon baya domin suma su nuna irin nasu bajinta ko kuma hazaka a duk fanin da suke bukata.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG