Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Da Wayar Hannu


Jama’a assalamu alaikum, a ci gaba da tattaunawar da muke a kowane karshen mako akan batutuwa da suka shafi rayuwar matasa maza da mata, satin da ya gabata mun duba yadda shafukan yanar gizo da iya kanta wayar hannu ke wa zumunci karan tsaye.

A wannan karshen makon zamu ci gaba ne da tattaunawa akan irin rawar da wannan fasahar zamani take takawa wajan gurbata rayuwar matasa duba da yadda iyaye daga bangarorin duniya da dama ke kokawa akan wannan lamari.

Makwanni kadan da suka gabata, dandalin voa ya sami zantawa da matasa maza da mata musamman akan yadda suke yawaita anfani da wayar hannu da kuma irin lokutan da suke amfani da it domin shiga shafukan yanar gizo, akasarin su kan yi amfani da ita ne wajan zantawa da juna musamman a shafukan sada zumunta na facebook, da Instagram da sauran su.

Matasa kan kwashe lokaci mai tsawo cikin dare suna hira da juna akan wadannan shafuka ba tare da yin la’akari da illar dake tattare da su ba. rashin samun isashshen bacci na iya hana matashi mayar da hankali wajan gudanar da ayyukan sa na yau da kullum, haka-zalika hasken wayar dake shigar masa ko matai do a lokacin da suke chatting duk nada illa ga lafiyar bil’adama.

Domin tofa albarkacin baki akan wannan batu da muke tattaunawa, ana iya ziyartar shafinmu na voahausafacebook domin bayyana ra’ayi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG