Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maitaimakin Shugaban Makaranta Ne Yayi Mata Ciki


Ma’aikatar ilimi ta jihar Neja ta baiwa mataimakin shugaban makaranta watau “Vice Principal” din makarantar sakandare Tunga dake a jihar Neja, Muhammad Muhammad, umarnin kula da dalibarshi da yayi wa ciki mai suna Faith Galadima, mai shekaru 16, da yaron da ta haifa har tsawon shekaru uku.

Jaridar Daily Post, ta rawaito cewe iyayen yarinyar sun kaiwa gwamnati kuka na neman dauki domin mataimakin shugaban makarantar wande kuma shi ke da alhakin daukan nauyinta da yaron da ta haifa ya yi watsi dasu.

Duba ga labarin haihuwar yarinyar, babban sakataren ilimi na jihar, Yahaya Garba yace ba’a kara wa malamin matsayi ba kuma ba’a kore shi daga aiki ba kuma ma’aikatar bata kare shi ta ko wane bangare ba, hasali ma an dakatar dashi daga aiki an kuma yanke kashi hamsin cikin dari daga albashin shi har zuwa lokacin da kotu zata yanke hukunci.

Ma’aikatar kuma ta tilasta wa malamin da ya dauki nauyin uwa da dan na tsahon shekaru hudu, kuma zata dubi lamarin bayan yanke hukuncin kotu. Babban sakataren ma,aikatar ilimin ya kara da cewa ma,aikatar ta dauki nauyin gwajin kwayoyin halittar da za ayi domin a yi saurin yanke hukunci a kotu. Yarinyar da iyayenta sun bayyana cewa a halin da ake ciki malamin ya gudu kuma basu san inda zasu same shi ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG