Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata A Fanin Siyasar Jamhuriyar Kamaru Ba A Barsu A Baya Ba


Gwagwarmayar mata a Kamaru
Gwagwarmayar mata a Kamaru

A Kamaru tawagogin mata na ta kai ziyara birane da kauyuka don karfafa gwiwar mata su shiga takara a matakai daban daban a zabukan kananan hukumomi da na majalisar dokoki da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa. Duk da yake mata sun kai rabin yawan al’ummar kasar, mata ba su ma kai daya bisa uku (sulusi) na yawan ‘yan majalisar Kamaru 180 ba, kuma su kashi shida cikin dari ne kawai na yawan masu mukamin magajin garin kasar wajen 380. Moki Edwin Kindzeka ya hada ma na rahoto daga birnin Yawunde (Yaounde) kan abubuwan zarge-zarge da ke hana mata shiga siyasa.

Moki ya saka sautin wata muhawara yayin da wata kungiyar gwagwarmaya mai suna More Women in Politics (wato Bukatar Karin Mata a Siyasa) ke kokarin shawo kan wani mutum mai suna Diedonne Kemche mai shekaru 62 ya bar daya daga cikin matansa shida ta shiga takara a zaben kananan hukumomin da za a yi.Ya

Kemche, wanda daya ne daga cikin ‘yan kabilar Bamikike masu auren mata da yawa, ya ce bai da tabbas din cewa matarsa na iya ayyukanta na cikin gida idan aka zabe a wani matsayi.

Da ya ke magana a harshen Faransanci, Kemche ya ce babu yadda za a yi matansa su bata lokaci wajen shiga harkokin siyasa. Kamata ya yi su mai da hankali wajen kula da yara, su rika aikace aikacen gona da na gida, da kuma uwa uba yin girki ma iyali da girmama mazajensu.

To ama matar ta Kemche mai suna Stephanie Ngogo, wadda malamar makarantar firamare ce, ba ta amince ba. Ta ce duk kuwa da rashin yadda mijin na ta, sai ta tsaya takarar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG