Zainab Sulaiman Umar ta san yadda ake neman kuri'a. 'Yar siyasar Najeriyar na zuwa gidaje, tana yada manufofin kamfen dinta da najam’iyyar ta.
Zainab ta tsaya a matsayin ‘yar takarar majalisa a Kano, wani birni dake a arewacin Najeriya. Ta na nuna kwarin gwiwarta da kuma fatan samun nasara, kuma da alamu al’ummar mazabarta na maraba da abin da take fada musu.
Sun yi imani da abin da nake yi
Zainab ta fadawa Muryar Amurka tawaya.
A cikin kasar da 'yan siyasa dattijai maza ne suka mamaye, Zainab ta fito fili. Ita mace ce. Mara aure. Kuma mai shekaru 26. Ga wasu masu jefa kuri'a a Nijeriya, wadannan kadai sun isa su hana ta shiga zabe.
Zainab ta yarda cewa mata ba sa shiga cikin siyasa a Najeriya, kuma mafi yawan mutane suna jin cewa bai kamata mata su tsaya takara ba.
A cikin ƙasar da maza suka mamaye komai, mazana rike da kashi 94 cikin dari na kujerun majalisu.
Amma yakin neman zabe ya bayyana wani abu na daban: dabi'u na canzawa, kuma mutane - mata da maza - sun fara amincewa mata su sami damar tsayawa takara.
Facebook Forum