Accessibility links

Masoya Kwallon Kafa Sun Barje Gumi Wajan Kwace Bindigar Wani Soja A Filin Wasa


Wasu hotunan bidiyo dake ta yawp a yanar gizo ya nuna yadda masoya kwallon kafa sukai ta gumurzu da wani soja a filin kallon wasan kwallon kafa a kasar Uganda.

Lamarin ya faru ne cikin wannan makon yayin da kungiyar kwallon kafa ta Onduparaka FC ke gwabzawa da kungiyar Saint.

Mujallar Daily Trust, ta wallafa cewa rahotanni sun bayyana cewar rudanin ya barke ne sa’ilin da kungiyar Onduparaka ta lallasa takwarar tata cikin minti 95 na kammala wasan.

Da ‘yan kallon wasan suka fara kuwwa kan nasarar da kungiyar Onduparaka, ta samu, sai sojan da ya rako kungiyar kwallon kafa ta Saint, mai dauke da bindiga mai sarrafa kanta kirar AK 47, ya yi wub ya gyara bindigarsa yana kokarin fara bude wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar sa ‘yan kallo suka far masa da kokowa har sai da suka kwace bindigar daga hannunsa.

XS
SM
MD
LG