Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta Yi Allah Wadai Da Cin Zarafin Pogba


Manchester United tayi Allah wadai da cin mutuncin da nuna wariyar launin fata ga dan wasan ta Paul Pogba, bayan da ya zubar da fanareti.

Kulob din kwallon kafa na Manchester United a yau Talata ya sanar cewa, yana kokarin gano mutanen da suka ci zarafin dan wasan ta Paul Pogba, ta yanar gizo, bayan da dan wasan tsakiya ya zubar da bugun fanareti a wasan da suka buga da kulob din Wolverhampton Wanderers, inda aka tashi da kunnan doki.

Pogba ya ci bugun fanarati bayan an kusa tashi daga wasan, sai dai kokarinsa bai cimma ruwa ba, bayan da mai tsaron raga na kolub din Wolves Rui Patricio, ya kare kwallon. Kunnan dokin ta sa United ta kasance a matsayi ta daya a teburin Premier, lamarin da ya kai ga dumbin magoya baya suka nuna wariyar launin fata ga ‘dan wasan ‘dan asalin Faransa.

A sanarwar da United ta fitar ta ce "Mutanen da suka bayyana wadannan ra'ayoyin ba su wakilci matsayin kulob dinmu ba, kuma muna bayar da kwarin gwiwa ga yawancin magoya bayanmu su la'anci hakan a kafafen sada zumunta", in ji United.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG