Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta Sayi Maguire Kan Kudi Pam Miliyan 80


Dan wasa Harry Maguire, (tsakiya)

“Ina mai farin cikin rattaba hannu a wannan kwantiragi na zuwa wannan mashahuriyar kungiya.” In ji Maguire, bayan da ya kammala komawa kungiyar ta United.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a Ingila, ta sayi dan wasa mai tsaron baya, Harry Maguire daga kungiyar Leicester City akan kudi pam miliyan 85 a cewar jaridar The Telegraph.

Hakan na nufin Maguire shi ne, dan wasa mai tsaron baya da ya fi tsada a duniya.

Bisa wannan kwantiragi, Maguire zai kwashe shekaru shida, inda yake da zabin kara shekara ta bakwai bayan ya kammala kwantiragin.

“Ina mai fari cikin rattaba a hannu a wannan kwantiragi na zuwa wannan mashahuriyar kungiya.” In ji Maguire, bayan da ya kammala komawa kungiyar ta United.

"Ina godiya ga duk wanda ya taka wata rawa a rayuwata ta kwallon kafa." Maguire ya rubuta a shafinsa na Twitter.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG