Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester City Tayi Rawar Gani ta Kai Dala Miliyan 544


Manchester City
Manchester City

A kakar wasa ta shekara 2013, kungiyar wasan kwallon kafa ta Manchester City, tayi hasaran Dala Miliyan 81, wanda ya hada da dala miliyan 25, da ta biya hukumar wasan kwallon kafa na Turai wato, UEFA, a matsayin tara.

A bana kuwa kungiyar ta Manchester City, ta samu rage hasaran da tayi, da fiye da rabi , inda harasa ya ragu zuwa dala miliyan 36, idan aka kwatantashi da hasaran bara.

Tun bayan sauya hannu da kungiyar, tayi na kumawa hannun , attajirin daular Larabawa, Khaldoon al-Mubarak, kungiyar, ta wuce adadin kudaden da aka shata mata zata kashe.

Al- Mubarak, yace kungiyar, tuni ta wuce dala miliyan 471, da aka shata mata inda yanzu, ta kai dala, miliyan 544. Yana mai cewa yanzu, za’a sake damawa da kungiyar a faggen wasa.

Manchester City 1'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00

XS
SM
MD
LG