Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makudan Kudaden Da Aka Biya Ɗiyar 'Yar Wasan Nollywood


A yayin da ake kaddamar da wani shirin talavijin na Adebua Tv wanda aka yi wa lakabi da “gaskiya” shafin mujallar Naija .com ya wallafa cewar shahararriyar ‘yar wasan kwaikwayon nan ta Nollywood da aka fi sani da suna Omotola Jalade ta yi bayani akan aurenta , da kuma bayyana ta hadu da mijinta da kuma irin makudan kudin da ‘yar ta ke samu a tallace tallace da take yi ma wasu kamfanoni.

‘Yar wasan kwaikwayon ta bayyana cewar na farko dai ta hadau da mijin nata ne a yayin da ‘yar uwar mijin nata ta hada su a wata coci kuma tun daga lokacin har ila yau tana zaune lafiya da mijin nata.

A lokacin da take bada amsoshin tambayoyin da aka yi mata dangane da adadin kudin da take samu, masu rubutu akan shafukan yada zumunci sun yi tunanin kwatankwacin kudi Naira miliyan dari biyu da hamsi, amm Omotola ta jijjiga su da mamaki.

‘yar wasan kwaikwayon ta bayyana cewar diyar ta mai suna Meraiah wadda ta yi ma kanfanin unilever talla, kanfanin ya biya ta kudi Naira miliyan biyu da dubu dari hudu a tallar magin da aka fi sani da suna dunkulen Knorr kadai.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG