Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maimakon Zaman Banza Ta Rungumi Sana'ar Dinki


Bilkisu Abdulkarim Ahmad

Wakiliyar DandalinVOA, ta samu hira da Bilkisu Abdulkarim Ahmad, matashiya mai sana’ar dinki, inda ta ce babban dalilin da yasa ta shiga sana’ar dinki, bai wuce rashin cika alkawari na teloli ba, da rashin biyan bukatar jama'a ta fannin dinki.

Ta ce shekara biyu kenan da ta fara wannan harkar, domin ganin tana da sha’awar dinki ya sa yayyinta suka bude mata shago, bayan da ta kammala karatunta na sakandire, tun da bata samu nasara a jarabawarta yadda ya kamata ba.

Bilkisu ta ce tana da burin cigaba da kara karatu nan gaba, amma tana yin sana'ar dinkin domin samun abun hannun ta kafin ta koma makaranta. Tace da ta bude shagon ta fuskanci kalubale da dama da ta kasance da ma’aikatan da ke karkashinta.

Ganin cewar ita mace ce kuma yarinya tana fuskantar matsaloli daga wajen abokan aikin nata, da kuma kwastamomi da suke kawo musu dinki, matsaloli irin na rashin yin dinki yadda suke bukata.

Daga karshe tace tana kira da jan hankalin matasa mussamman mata da su zama masu dogaro da kai, su kuma jajirce wajen neman nasu na kansu.

Ga tattaunawar wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG