Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Ke Sa Wasu Samari Neman 'Yan Matan Abokan Su


A shirin namu na yau, mun sami jin ra'ayoyin wasu matasa ne maza da mata dangane da dalilan da ke sa wasu daga cikin su ke kyashin abokan soyayyar su harma a wasu lokuta sukan kai ga neman sauya sheka! wato kawai sai kaga saurayi ko budurwa ta bar saurayinta ta koma ma abokin saurayin.

Babban abin da yawancin jama'a ke tunani anan shine kwadayin abin duniya, kamar yadda wasu da dama suka bayyana, koda shike kowa da irn nasa ra'ayin mabanbanci da na saura.

Daya daga cikin matasan da muka zanta da shi ya bayyana mana cewar hakan ya taba faruwa da shi, wato yana da budurwar da yasa rai zai aura amma sai aka sami akasi a sakamakon yaudarar da abokin nasa ya yi masa. Matashin ya kara da cewar ba matsalar kudi ko wani abin duniya bane, iya magana ne da karya yasa har ya kaiga hure mata kunne.

Haka kuma daya cikin 'yan matan da suka bayyana nasu ra'ayin, ta ce babban dalilin da ke haifar da irn wannan matsala itace rashin hangen gaba da kuma sanin ciwon kai. matashiyar ta ce yawancin 'yan mata na dora ra'ayin su ne akan samari masu abin hannu domin kuwa babu macen da ke so ta wahala.

ga cikakken shirirn..Dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG