Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai gidan Tauraruwa Celine Dion ya Rasu


Shahararriyar mawakiyar nan mai su a Celine Dion ta rasa mai gidanta Rene Angelil sanadiyar cutar daji, wanda ya yi shekaru 73 a duniya.

A jiya alhamis ne Celine Dion ta sanar da rasuwar mai gidanta, kuma nan da ‘yan kwanaki za a sami karin bayani a shafin ta na yanar gizo.

Mr. Rene dai shine manajan Celine Dion kafin rashin lafiyarsa ta kaishi kasa, ya fara haduwa da ita lokacin tana da shekaru 12 kuma ya kula da harkokinta na waka har zuwa lokacin da ta shahara, a shekarar aluf dari tara da tasa’in da hudu kuma suka yi aure inda aka yi wani kasaitaccen shagali a Notre Damme, Basilica.

Celine Dion tare da mai gidanta suna da ‘yaya maza guda 3 Rene Charles dan shekaru 14, da tagwaye Nelson da Eddy ‘yan shekaru 5 da haihuwa.

A sahekarar aluf dari tara tasa’in da tara ne aka gano cutar da ke damun Mr. Angelil, abinda ya sa Celine Dion ta taka burki a harkokinta don ta kula da mai gidanta a shekarar 2014. Celine Dion ta fadi cewa daga baya Mr. Angelil ya bata goyon bayan cigaba da harkokinta.

Magajin garin Montreal, asalin garin Mr. Angelil, ya yaba wa marigayin akan cewa “mutum ne wanda bai taba mantawa da inda ya fito ba”.

A shekatrar 2014, Angelil ya sauka daga mukaminsa na manajan Celine Dion ya ba wani amininsa don ya cigaba da kula da harkokinsu, amma duk da haka, Angelil ya cigaba da bada gudunmuwarsa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG