Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mage (Kyanwa) Ta Zama Miloniya A Amurka


Mage Nala da mai ita Varisiri a dandalin Steve Harvey Show.
Mage Nala da mai ita Varisiri a dandalin Steve Harvey Show.

Attajira Varisiri Methachittiphan dai kaura ta yi zuwa Amurka, inda labarin nasarar da ta yi a rayuwa ya zama wani abin kwatance da koyi. Ta fara rayuwa a Amurka ne kamar sauran dalibai ‘yan kasar Thailand, cike da marmarin samun ilimi da kuma sabuwar rayuwa. Ana nan sai ta dauko wata kyanwa ‘yar watanni 5 mai suna ‘Nala’ daga wuraren tsugunar da dabbobin da aka tsinta ko wadanda ba su da masu kula da su a California. Abin da ya biyo baya ta kafar intanet kuwa tamkar mu’ujiza ce. Warangkana Chomchuen na Muryar Amurka ya hada ma na wannan rahoton.

Warangkana ya ce Nala na yawan son wasa da kwalaye. Ta cika son bacci cikin kwali amma kuma ta tsani ta samu kanta a gefen kofa. Ta na kara tamkar dai duk wata kyanwar da ke duniya, sai dai kawai ita daban ce. A duk duniyar nan babu kyanwar da ta kai ta shahara ta kafar intanet, inda ta ke da masu kallo sama da miliyan hudu a kafar Instagram, kuma ta samo ma mai ita miliyoyin daloli.

Hakika, shaharar Nala ta canza rayuwar mai ita kwata-kwata, daga wata ‘yar asalin kasar Thailand wadda ta kammala jami’a a Amurka zuwa wata hamshakiyar attajirar ‘yar kasuwa – albarkacin amfani da kafar sada zumunta.

Varisiri Methachittiphan mai kyanwa Nala, ta bayyana cikin harshen Thailand cewa, “Ban taba tsammanin kyanwata za ta samu magoyo baya har miliyoyi ba. Kai, ban ma taba tunanin cewa zan yi wannan har na tsawan shekaru biyar ba.”

Bayan da Varisiri ta yi ta nuna yadda ta ke ma’amala da Nala har ta samu ‘yan kallo da dama, sai kamfanonin yin kayan wasan dabbobin gida irinsu kyanwa da karnuka da dai sauransu su ka shiga biyanta makudan kudade ta na wasa da kayansu don kwatanta ma masu kallo ingancin kayansu. Varisiri ta kuma shiga tallata kayan abincin dabbobin gida da dai sauransu. Ta haka ta zama hamshakiyar mai kudi albarkacin wannan mage.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG