Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mafita Ita Ce Al'umma Ta Yi Marhaba Da Sayen Fayafaye Ta Halartacciyar Hanya


Sadiq M. Mahabir
Sadiq M. Mahabir

A shirinmu na nishadi yau mun sami bakuncin Sadiq M. Mahabir wanda ya ce sha'awa ce da son fadakarwa tasa shi shiga harkar waka, bayan da mawaka kamar su Nazifi Asnanic, suka sa shi kaimin wajen cimma muradunsa

Ya kara da cewa ya zabi wakokin soyayya domin nan ne matasa suka fi raja'a kuma ta wannan hanya yake isar da sakonin zamantakewa na yau da kullum.

Matashin ya kara da cewa banda wokokin soyayya yakan waiwaiyi wasu bangarorin rayuwa duk a yunkurin fadakarwa da kuma nishadantarwa.

Mahabir ya bayyana cewa tun lokacin da ya fara waka bai taba fuskantar wani kalubale daga bangaren iyaye ba illa wasu ‘yan matsaloli da ba’a rasa ba a fuskar al’umma.

Daga karshe ya kara da cewa bukatar kowane mawaki kamarsa ita ce al’ummar gari ta yi marhaba da wakokinsu ta hanyar sayen fayafayansu ta hallartaciyyar hanya maimakon barauniyar hanya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG