Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Leicester Ta Koma Ta Biyu


Leicester City na murnar nasarar da su ka yi a karawarsu da Everton

Bayan da ta rasa matsayi na biyu, kulob din Leicester City ta sake yin nasarar komawa kan wannan matsayin albarkacin wata kwallo da dan wasanta Kelechi Iheanacho ya ci a kurarren lokaci, inda aka tashi da 2 – 1 a gwabzawar da aka yi ranar Lahadi a gasar Premier League.

Jamie Vardy ya ciwo kwallo ma Leicester a minti na 68, bayan da Richarlison ya yi nasarar sa Everton ta tsere ma Leicester da farko. Ci na shida a jere da ‘yan wasan da ke karkashin kulawar koci Brendan Rodgers ya sa sun zama masu kare kanbunsu kuma na biyu.

An ce saura kiris kocin Everton wato Marco Silva ya rasa aikinsa a farkon makon saboda ci biyu kawai yaransa su ka yi a Garawa 10 da aka yi, al’amarin da ya kawo kashe gwiwa. Sannan kuma ga wannan al’amari na baya baya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG