Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwanakin Eden Hazard A Chelsea Sun Kusa Karewa?


Eden hazard
Eden hazard

Watanni 12 da suka shige, babu wani dan wasan tamaula da ‘yan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea suke dauka a zaman dan lelensu kamar Eden Hazard. Ya taka muhimmiyar rawa wajen jagoranci ma kulob din don lashe kofin lig na Firimiya na Ingila, kuma a lokacin, dukkan alamu sun nuna cewa zai bi sahun ‘yan wasa irinsu Didier Drogba da Petr Cech a matsayin taurarin da Chelsea ba zata taba mancewa da su ba.

Amma a bayan da aka yi ta yi masa ihun nuna tsana jiya laraba a lokacin da aka fitar da shi daga wasan da suka yi da PSG, da alamun cewa watakila dan wasan dan kasar Belgium ba zai saka rigar kwallo ta Chelsea a kakar kwallo mai zuwa ba. A zahiri dai, bai yi wasan azo a gani ba.

A farkon kakar kwallo ta bana dai, an danganta rashin kokari da kuzarinsa a filin wasa a kan dangantakarsa da ta yi tsami da manajan Chelsea a wancan lokaci, Jose Mourinho, kuma a lokacin ba ma shi kadai ne ba ya wasa yadda ya kamata ba.

Amma a bayan da aka kori Mourinho, ‘yan wasa irinsu Diego Costa da Cesc Fabregas sun farfado suna nuna bajimta a filin wasa, amma har yanzu, Hazard baya nuna wata bajimta a filin wasa.

Kafin karawarsu ta farko da PSG a gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai, Hazard yace zai yi wuya yayi watsi da duk wani tayin da zakarun na kasar Faransa zasu yi masa na yaje ya buga musu kwallo, abinda magoya bayan Chelsea da yawa suka dauka a zaman alamar cewa zamansa a kulob dinsu ya zo karshe.

A wasansu na jiya da PSG, Hazard dan wasan PSG Angel Di maria sun yi musanyar riguna, abinda ya harzuka magoya bayan Chelsea suka rika yi masa ihu na tur. Wannan abu da yayi, ya kuma nuna cewa ransa ba ya kan wasan na jiya. Masana suka ce a zahiri, a wannan lokaci kuma, kungiyar Chelsea ba ta bukatar ‘yan wasan da zasu shiga fili zuciya da hankulansu suna wani wurin dabam.

Masu fashin bakin tamaula sun ce watakila Hazard ya koma Real madrid ko PSG, amma suna ganin salon wasansa a yanzu zai fi dacewa da Real madrid.

XS
SM
MD
LG