Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Orphans And Women Support Foundation Ta Koyawa Mata Sana'oi A Jihar Kano


Kungiyar tallafawa mata da marayu wato Orphans and Women Support Foundation, kungiya ce mai zaman kanta da ke taimakawa mata da marayu mussamam a cikin halin kuncin rayuwa da Najeriya ke fuskanta .

Shugaban kungiyar A’isha Datti Abubakaar, ta ce suna koya wa mata sana’oi a kalla guda goma domin su zamo masu dogaro da kai.

A’isha Datti Abubakar, ta bayyana cewa a yanzu haka dai suna da kudirin taimakawa mata dari biyar, bayan koya musu sana’oin dogaro da kai, kungiyar zata basu kayan aiki domin su zamo suna sana’antarwa tare da karbar kayan nasu domin sayar musu tare da tallata su.

Ta kara da cewa burin kungiyar tasu dai bai wuci su ga mata sun zamo masu dogaro da kai ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:31 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG