Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Matasan Iwere Ta Zargi Wasu 'Yan PDP Da Suka Canza Sheka Da Neman Gamawa Da Kabilar Ijaw


Wata kungiyar wanzar da zaman lafiya ta matasa da ake kira Iwere socio-cultural organization a yankin Niger Delta, ta yi kira ga gwamantin tarayya da ta sa a daina kama, da wulakanta matasan kabilar Ijaw da ke wannan yankin, musamman ma a garin Warri. Kungiyar tace wannan matakin na haddasa rigingimu a yankin.

Haka kuma kungiyar matasan ta musanta zargin da ake wa tsohon shugaban ‘yan bindigar yankin na cewa da hannunsa a harin bom din da aka kan bututun man petur da kuma sace wani dan jarida da aka yi a cikin shekarar da ta gabata. Kungiyar kuma ta zargi wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar PDP da su ka canza sheka zuwa APC da kokarin gamawa da ‘yan kabilar ta Ijaw.

A wata sanarwa da kungiyar matasan ta fidda, wadda Mr. Merie Oritsejolomi da Johnbull Deghelli Omadeli su ka sanyawa hannu, sun yi kira ga jami’an tsaro da su binciki wadanda suka lalata bututun man petur din ba kama matasan kabilar Ijaw ba da basu san hawa ba basu san sauka ba.

XS
SM
MD
LG