Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwallon Kafar Kasar Holland Ta Yi Babban Bako


Ronald Koeman
Ronald Koeman

An bayyana sunan tsohon mai horar da ‘yan wasan kungiyar Everton Ronald Koeman a matsayin sabon mai kula da ‘yan wasan kasar Holland.

Koeman mai shekaru 54, da haihuwa ya rattaba hannun bisa yarjejeniya kwantirakin shekaru hudu da rabi inda zai karkare a shekara 2022, ya maye gurbin Dick Advocaat, ne wanda ya ajiye aikinsa bayan da ya gaza kai kasar gasar cin kofin duniya da za ayi a kasar Rasha a shakarar nan ta 2018.

Ronald Koeman ya takawa kasar ta Netherlands leda ya kuma rike kungiyar kwallon Kafa ta Everton kafin nan ta Sallami meshi a watan Oktoban 2017 bayan da kungiyar ta kasa tabuka wani abun kirki a gasar Firimiya lig na kasar Ingila.

Koeman zai fara wasansa na farko da tawagar kasarsa ta Netherlands a wasan da zasu kara da kasar Ingila ranar 23, ga watan Maris, shekara dubu biyu da sha takwas, (2018).

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG