Sa'oi kadan bayan an cereta daga gasar cin kofin zakarun turai Uefa Champion league na 2018/19, a matakin wasan zagaye na biyu Kungiyar kwallon kafa ta AS Roma ta sallami kocinta Eusebio Di Francesco. Shugaban kungiyar ta Roma, James Pallota shi ya sanar da matakin koran kocin bayan wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki a kungiyar da shugaban ya jagoranta.
Kocin Di Francesco, ya karbi ragamar horar da kulob din Roma ne a watan Yunin shekara 2017, har zuwa lokacin da kungiyar ta sallameshi. Kaftin din kungiyar Danele De Rossi ya bayyana cewar yan wasanta sun bayyana goyon bayansu gare shi. A nasa ran cewar tsohon kocin Leicester City, Claudio Ranieri shi zai maye gurbin Di Francesco domin jagorancin horar da kungiyar.
Shima Ranieri ya taba horar da kungiyar ta AS Roma daga watan Satumba na shekarar 2009 zuwa Fabarairu na shekarar 2011.
Roma dai tayi wasane tsakanita da FC Porto, a ranar laraba in data sha kashi daci 3-1 a haduwarsu ta biyu sai dai akarawar farko Roma a gida ta samu nasara daci 2-1 amman hakan bai bata damar hayewa zagayen gaba ba sakamakon jimillan kwallaye Porto tana da 4 ita kuwa Roma 3.
Facebook Forum