Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwallo Ta Monaco Ta Sallami Kocinta Leonardo Jardim


Kungiyar Kwallon Kafa ta Monaco da ke Faransa ta kori kocinta, Leonardo Jardim, sakamakon rashin tabuka wani abu da kungiyar ke fuskanta a wannan kakar.

Monaco ita ce ta uku a can kasan teburin gasar Lig 1, Jardim ya taimaka wa Monaco lashe gasar Lig 1 a shekarar 2017, wanda shi ne karon farko tun
shekarar 2000.

Kocin ya kuma taimaka wa kungiyar wajen kaiwa matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai na shekarar 2016-2017.

Kazalika ya taimaka wa wajen gina ‘yan wasa irinsu Kylian Mbappe da yanzu haka ke taka leda a PSG. A shekarar 2014 ne Monaco ta kulla kwantiraki da Jardim mai shekaru 44.

Inda ake ganin Thierry Henry, ne zai maye gurbin Jardim don ci gaba da horar da ‘yan wasan na Monaco. Thierry Henry ya fara buga wasansa a matsayin dan wasan gaba na gefen hagu, kuma ya zura kwallaye 28 a wasanni 141 da ya fafata wa Kungiyar Monaco.

Kuma tsohon danwasan kasar Faransa ne wanda suka lashe gasar cin kofin duniya na 1998, ya zura kwallaye fiye da 400 a yayin da yake taka leda, ya samu nasara a kowane babban kulob din da ya buga mata wasa tun daga Monaco, Arsenal, Barcelona, da kuma Juventus.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG