Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar D'Tigress Ta Lashe Gasar Kwallon Kwando Ta Afirka


Tawagar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D'Tigress, sun doke takwararsu ta kasar Senegal domin ci gaba da zama zakarun kwallon Kwandon mata ta Afrika.

Tawagar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D'Tigress, sun yi nasarar kare matsayinsu na zama zakaran gasar wasannin kwandon Mata ta FIBA, kofin da suka sami nasarar lashewa shekaru biyu da suka gabata.

A wasan karshe da aka buga ranar Lahadi, filin kwallon Kwando na Dakar, wanda ya dauki 'yan kallo sama da dubu 15, matan Najeriya sun doke Senegal ne da ci 60-55, inda suka lashe kofin gasar sau biyu a jere.

Da wannan nasara da suka samu ranar Lahadi, D'Tigress ta zama kungiya ta farko da ta fara cin kofuna biyu a jere a gasar FIBA ta Mata, tun lokacin da Angola ta yi nasarar a shekarar 2011 da 2013.

Najeriya ta doke kasar Tunisia da ci (75-26 ), Kamaru da ci (106-39), jamhuriyyar demokradiyyar Congo da ci (79-46), Mali da ci (79-58) da matsakaicin maki 42.5, yayin da Senegal ta doke Cote d'Ivoire da ci (77-36), Egypt da ci (85-47), Angola da ci (88-54) da Mozambique da ci (60-57) da tazarar maki 29.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG