Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kulla Auratayya Tsakanin 'Ya'ya Da Ake Ada Na Daga Cikin Dalilai Na - Inji Muktar


Mafi yawan fina-finai na, ina duba matsalolin zamantakewa ne, mussaman ma ta Malam Bahaushe, inda a fim din da nake aiki a yanzu na waiwayi matsalar karancin zumunci kamar yadda Bahaushe ke yi a da, na kulla auren zumunci a ta bakin Muktar Isa, mai shirya fina-finai.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir. Muktar ya ce ya shafe fiye da shekaru 10 yana masana’antar kannywood, kuma ya fara harkar fim ne tun daga tushe, inda ya ce a yanzu ya fi maida hankali a fina-finan gidajen talabijin.

Muktar ya kara da cewa a da Bahaushe kan kulla auratayya tsakanin ‘yayansa da na ‘yan uwansa inda iyaye kan nema wa ‘ya’yansu aure, a yanzu wannan al’ada na neman gushewa hakan ne ya sa fim din sa ya maida hakanli akan wannan batu inji Muktar Isa.

ya ce rashin raya al’ada ne ya sa matasa mussamam ma mata kan jima a kasa ba tare da sun sami mazajen aure ba, a bangaren maza kuma sai ka ga suyi zabin tumun dare, wato su zabi macen da ba ta da tarbiyya wadda hakan na daga cikin dalilan da susa sa Muktar ya kalli wannan matsala har ya shirya sabon fim din sa.

A cewarsa, hanya mafi sauki ta wayar da kan al’umma ita ce ta fina-finai kuma a nuna fina-finan a gidajen talabijin domin ta haka ne jarumai suke mai da kudaden da suka kashe a yayin shirya fim, da kuma samar da hanya kwakkwara domin kauracewa da magance masu satar fasaha.

Daga karshe ya bayyana cewa daga cikin kalubalen da suke fuskanta a masana’antar fim dai bai wuce rashin samun tallafi daga masu zuba hannun jari ba a sakamakon wasu dalilai nasu, da rashin tallata hajar su ga al'umma duk suna daga cikin abinda haifar da koma baya ga harkar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:34 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG