Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli ta Abuja ta Yanke Hukuncin Gaggauta Rantsar da Tsohon Mataimakin Gwamna Jihar Taraba a Matsayin Gwamna.


Babban Kotun Abuja
Babban Kotun Abuja

Kotun koli ta Abuja, ta yanke hukuncin , cewar a rantsar da tsohon mataimakin Gwamnan jihar Taraba, Alhaji Sani Danladi, wanda aka tsige, a matsayin Gwamnan jihar Taraba , da gaggawa.

Biyo bayan wannan hukuncin da kotun ta zartar, a yau din nan, an dauki matakan ko ta kwana a Jalingo, fadar jihar Taraba, kakakin rundunar ‘yan Sandan Jihar, ASP Joseph Kwaji, ya bukaci jama’a, su kasance masu bin doka da oda .

Daya daga cikin Lauyoyin da suka kare tsoho mataimakin Gwamna, Barrister, Dalung, yace hukuncin da kotun, ta yanke zai hana , tsige-tsige ba’a bisa ka’ida ba nan gaba.

Shugaban Jamiyar adawa , ta APC, Alhaji Hassan Jika Ardo, ya nuna farin ciki dagane da hukuncin da kotun ta zartar, da kuma kira da a tabbatar da cewa duk wanda aka tsige, a bisan zalunci, kotu ta maida shi.

A na iya sauraron sauti domin jin cikkaken labarin.

Gwamnan Jihar Taraba - 4"48"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:48 0:00

XS
SM
MD
LG