Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Tayi Watsi Da Shari'ar Bill Cosby Akan Fyade


Bill Cosby
Bill Cosby

Wani alkali a nan Amurka ya watsar da shari’ar da aka yi ta mashahurin dan wasan barkwanci nan na Amurka Bill Cosby wanda aka tuhuma da laifin yin fyade, a bayan da gungun masu bin Kadin shari’ar su 12 suka kasa daidaitawa a tsakaninsu kan laifi ko rashin laifinsa.

Masu bin Kadin shari’ar sun shafe awa 50 suna muhawara tsakaninsu ba tare da cimma daidaito ba a garin Norristown na Jihar Pennsylvania, dangane da tuhumar da aka yi ma Cosby cewa yaba wata mata wani magani ta sha yayi mata fyade a shekarar 2004.

Nan take masu gabatar da kara suka ce zasu sake gurfanar da shi a gaban kotu, kuma har yanzu yana fuskantar tuhumar aikata laifuffuka uku na yin fyade.

Cosby yayi suna da wani shirinsa na telebijin da aka yi shekara da shekaru ana nunawa mai suna The Cosby Show.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG