Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Amince Da Bukatar Shah Rukh Khan


 Shah Rukh Khan
Shah Rukh Khan

Babbar kotun jihar Gujarat dake kasar Indiya ta dage sauraran karar da hukumar ‘yan Sandan tashen jiragen kasa na Vadodara dake kasar ta Indiya ta shigar wace ta bukaci a baiwa shararren jarumin fina finai nan na Bollywood watau Shah Rukh Khan, sammace akan mutuwar wani mutun a tashar jiragen kasa a lokacin da ake tallatar da wani fim da jarumin ya fitar mai suna Raees.

Mai shara’a, J B Pardiwala, ya amince da wannan bukatar ta lauyan Shah Rukh Khan, na kin amincewa da bukatar ta hukumar ‘yan Sanda na cewa Shah Rukh Khan, ya hallara a ofishin ‘yan Sanda domin bada ba’asi akan abinda ya faru a lokacin da ake tallatar da fim din a tashen jirgin.

Lauya mai kare Shah Rukh Khan, Salil Thakore, yayi gaddamar cewa karkashen doka ‘yan Sanda basu da hurimin baiwa Shah Rukh Khan sammace domin baya zaune kusa da harabar ofishin ‘yan Sandan .

Fahreed Khan Pathan, mazaunin yankin ya gamu da bugun zuciya abinda ya yai sanadiyar mutuwarsa a lokacin da yake kokarin ganin jarumin, a ranar 23, ga watan Janairun wannan shekarar a lokacin da ake yawon tallatar da fim din Raees.

An dai bukaci Shah Rukh Khan, da ya biya iyalan mamamci diyya, wasu masu fafutuka kuma sun bukaci wata kotun magistrate da ta tuhumi shah Rukh Khan da laifi, kotun ta bukaci hukumar ‘yan Sandan da ta shigar da takardun neman hakkan, amma kawo yanzu ba a shigar da wasu takardun ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

XS
SM
MD
LG