Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Kudu ta Sha Kashi


 Islam Slimani dan wasan Algeria
Islam Slimani dan wasan Algeria
A ci gaba da gasar cin kofin kwallo kafa ta duniya, Algeria ta rangadawa Koriya ta kudu kashi da ci 4 da 2 a karawar da suka jiya.

Wannan nasaran da Algeria ta samu yasa ta a mataki na biyu a rukunin da take.
Rabon da Algeria, ta samu irin wannan nasaran a gasar cin kofin kwallo kafa na duniya tun shekaran 1982 kimmanin shekaru 32 kennan.

Algeria de itace kadai kungiyar kwallon kafa daga nahiyar Afirka da ta cin har kwallaye 4 a gasar ta bana kawo yanzu.

‘Yan wasan na Algeria suka ce sun bi umarni mai kula da kungiyar tasu ne shi ya kawo wannan nasaran.

Daga fara wasan Algeria ta mamaye wasan har na tsawon minti 15 ta maida Koriya ta kudu abun wasa.

Idan har koriya ta kudu tana son tayi rawar gani to sai fa ta doke kungiyar kwallon kafa ta Belgium wace itama ba kanwan lasa bane.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Direct link
XS
SM
MD
LG