Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shawarwari ga Matasa Akan Sana'o'i


A fannonin al'umma daban da ban, mata suma suna taka muhimmiyar rawa kamar siyasa, ilimi da kasuwanci. Wata mace mai kamar maza na bada shawarwari ga matasa akan irin sana'o'in da suke sha'awa.

Mata suma ba a barsu a baya ba a fannin kasuwanci, kamar yadda wata mace ke ba ‘yan kasuwa da matasa shawarwari akan yadda zasu fara gudanar da ayyukansu, domin samun cigaba mai amfani.

Ita dai matar mai suna Malama Zahida Mahadi Jibiril, tana da kamfanin dake yin nazari, da bincike da kuma bada shawarwari akan sana’o’I ga duk mai sha’awa, don iya gano ko sana’ar na da riba ko akasin haka. Da kuma taimaka wa da hanyoyin samun jari ga mai bukata.

Malama zahida tayi kira ga matasa dasu yi bincike akan duk wata sana’a da suke da sha’awar yi, don sanin amfanin ta ko kuma akasin haka.

Ga wakiliyar Dandalin VOA da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG