Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwaci Ta Yanar Gizo Tafi Riba Da Masu Saye


Sadiya Muhammad

Daga cikin kalubalen da nake fuskanta kasancewa ta mace, kuma wacce take yawan amfani da shafin sadarwa domin harkar kasuwanci na, akan yi mana kallon marasa kamun kai, sakamakon kullum ana ganinmu online da zarar an yi mana magana za’a same mu a shafin sadarwar.

Ko da yake mafi yawan al'umma basa la’akari da cewar shafin facebook, da sauransu shafukan suna da amfani ta yadda mutum yayi niyya, kama daga neman abokai ko domin gudanar da kasuwanci.

Malama Sadiya, ta ce duk me son kayanta da zarar ya zaba a shafinta na facebook, takan yi kasuwanci da shi ta hanyaramfani da facebook, suyi ciniki har su tsayar da farashi, duk yadda suka amince sannan sai a aika wa mai saye a duk inda yake ta hanyar turawa tashoshin motocin haya.

Sadiya Muhammad, dai tana sayar da atampopi, shadda da leshi, da kuma kayan maza zannan ta ce tana odar takalma ne daga kasar Malaysia, domin sayar da su a kan shafukan sadarwa na facebook.

Kana akwai damar yin cinikayya kafin ta sallamawa mai saye duk a shafin na facebook.

Ko da yake da farko tana da shago a cewarta, amma dole ta sanya ta canza salo inda ta fara tallata kayanta ta kafar sadarwa, ta kuma lura ya fi shagon samar da masu saye.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG