An umurci kamfanin Facebook da ya daina tattara bayanan masu anfani da shafinsa a kasar Jamus bayan hukuncin da wata kotu ta yanke a ranar Alhamishin nan na cewa kamfanin sada zumunta mafi girma a duniya na cin zarafin masu amfani da shi a kasar, ta hanyar tattara bayanansu ba tare da izininsu ba.
Kasar Jamus, wacce ke daukar lamarin kare sirrin al’umma da matukar muhimmanci, na sahun gaba wajen la’antar kamfanin Facebook, bayan abin kunyar da kamfanin Cambridge Analytica yayi a shekarar da ta gabata, inda ya tona assirin tarihin rayuwar milyoyin masu anfani da Facebook ba tare da yardarsu ba.
Hukuma mai sanya ido kan aiyukkan kamfunna da masana’tu, ta nuna rashin amincewarta akan yadda Facebook din ke zuko bayanan jama’a daga wasu manhajojinsu na daban kamar su WhatsApp da Instagram, da sauran hanyoyinta na duniyar gizo ta Internet wajen leken asiri, abun yakan shafi har ma wayanda basa amfani da manhajar dake nuna sha’awar su ko suke musayar wasu abubuwan dake shafukkan.
“
A nan gaba, ba za’a sake kyale Facebook ta rinka tilastawa masu anfani da shafukkanta su aminta da akidar tara bayanansu ko ko kuma saka bayanan da ba’a samo daga Facebook din kanta a cikin shafukkan jama’ar ba
inji shugaban Hukumar Kula da Ka’idodjin Aiyukka na Tarayya, Andreas Mundt.
Facebook Forum