Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Indiya Zata Aika Wasu 'Yan Sama Jannati


Kasar Indiya zata shiga cikin jerin kasashe a duniya da suka aika jirgin sama mai sarrafa kansa cikin duniyar wata, firaministan kasar Narendra Modi, ya bayyana hakan yau da cewar idan Allah ya kai rai shekarar 2022, kasar zata aika nata jirgin.

Kasar zata bi sahun kasashe kamar su Amurka, Rasha da China, zasu aika ‘yan sama jannati duniyar wata wanda zasu aika maza har da mata, wadanda suka kware a aikin.

Rakesh Sharma, shine ba indiye na farko da ya taba zuwa duniyar wata, a jirgin ‘Soviet rocket’ a shekarar 1984, kasar ta indiya ta aika na’urar tauraron dan’adam kusa da duniyar Mars a shekarar 2014.

Kasar indiya ta samu ‘yancin kanta daga mulkin mallaka na Ingila a shekarar 1947. An dai yi gwajin jirgin da zai tafi duniyar ta wata, a 'yan kwanakin baya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG