Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Kasar Taiwan Yace Zai Samar Da Isassun Manhajoji Ga Apple


Shahararren kamfanin kasar Taiwan wanda ya shahara wajen kerama kamfanin Apple wasu manhajojin, ya bayyana cewar ya shawo kan matsalar satar bayanai da aka samu a kamfanin, wanda hakan ya ba ‘yan kutse damar satar bayanai a wayoyin Apple.

Hakan yasa kamfanin rufe wasu sassa na kamfanin don kokarin shawo kan matsalar, ana kai hari akan akan sashen dake hada wani bangare mai muhimanci a wayoyin iPhone, kamfanin ya musanta cewar da akayi an shiga cikin yanar gizon kamfanin.

Shugaban kamfanin Wei, ya gayama manema labarai cewar wannan hari da aka kai ya bashi mamaki, ya kara da cewar mutane kan yi kuskure kuma sun iya shawo kan matsalar, kamar yadda shafin yanargizo na kafar sadarwar BBC ingilishi, ya wallafa.

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG