Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Google yayi Aman Dala 2,250.


Kamfanin fasaha na Google ya biya dala $2,250 domin nuna tsaraicin wata mata dayayi alokacin da take zaune a kofar gidanta.

A kan shafin google na kan yanar gizo a kwai majahar taswira mai nuna hotunan gidaje da hanyoyi, wanda idan aka rubuta adireshi akan mahajar to zata bayyana hotan gidan harma da titin kofar gidan.

A shekara ta 2011 ne dai wata mata mai suna Grillo tare da abokan aikinta sukasa adireshin gidan ta a majahar google sai hotan gidan ya bayyana da hotan Grillo zaune a kofar gidan batare da tasa kayan kirki a jikin taba.

Bayan shekara biyu matar ta yanke hukuncin daukar kamfanin google zuwa kotu, domin kamfanin ya jefata cikin wani hali na damuwa kasancewar kowa zai iya budewa ya ganta cikin hotan, duk dayake abokan aikin ta sun riga sun gani.

Grillo ta nemi kotu data karba mata $45,000 daga kamfanin amma alkalin dai ya yankewa google hukuncin biyan $2,250 da kuma $159 kudin data kashe na kara.

Alkalin dai yace duk da cewa mutane na waje inda kowa zai iya ganinsu wannan bazai baiwa kowa damar ace an bude tsirrin mutane ba.

XS
SM
MD
LG