Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Apple Na Shirin Wata Sabuwa


Ana sa ran shahararren kamfanin wayar hannu Apple, zai kaddamar da wata sabuwar waya kafin karshen wannan shekarar da muke ciki, kuma ana sa ran sabuwar wayar zata fito da sababbin nau’uka daban daban.

Daga cikin sababbin nau’ukan da wayar zata fito da su sun hada da launuka kamar su launin ruwan gwal da fara da ja da baka da mai launin ruwan lemu da ruwan hoda, kuma fadinta zai kai inci 6.5, da kuma mai fadin inci 6.1.

Wannan na nufin cewa Kamfanin Apple, zai kara kaloli a cikin wadanda yake da yawan amfani da su koda shike bai taba yin waya mai launin ruwan lemu ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG