Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kada Mu Yi Kasa A Gwiya Wajan Neman Ilimi-Inji Zulaifa


Zulaifa Hussaini
Zulaifa Hussaini

Kasancewar ta 'yar asalin Nijeriya, yasa na rasa samun gurbin karatu a kasar Ghana, domin samun damar zama likita inji wata matashiya Zulaifa Hussaini.

Zulaifa ta bayyana haka ne a yayin zantawa da DandalinVOA , inda ta ce ita ‘yar asalin garin Kura ce amma zama ya kai iyayenta kasar Ghana, kasuwanci inda aka haife ta, har ta yi makarantar firamare da sakandire a can amma samun gurbin jami’a ya ci tura.

Ta kara da cewa sai da ta shafe fiye da shekaru uku tana neman gurbin karatu bayan kammala karatun sakandirenta a can duk kuwa da cewar ta samu nasara a jarabawarta.

Zulaifa ta ce kasancewar tana sha’awar karatu ne ya sa ta dawo gida domin sake sabon lale na karatu bayan da ta jaraba wasu sana’oi a can Ghana, inda zaman aurenta ya gagara dorewa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG