Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Juventus Na Kokarin Shiga Gaban Manchester United Da Arsenal Wajan Sayen Nemanja


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kammala sayen dan wasan tsakiya na Real Betis mai suna Dani Ceballos akan kudi yuro miliyan €18.

Barcelona da Benfica sun cimma yarjejeniya wajan sayen dan wasan baya na Benfica Nelson Semedo dan shekara 23 da haihuwa.

Watford ta sayi Nathaniel Chalobah, daga kungiyar Chelsea, na tsawon shekaru biyar.

Real Madrid ta saka fam miliyan £60 don ganin ta kawo mai tsaron raga na Manchester United, David De Gea.

Manchester City da Real Madrid sun jera sahu daya wajen sayen matashin dan wasannan MBappe mai shekara 18 da haihuwa.

Juventus, tana kokarin shan gaban Manchester United da Arsenal wajan sayen Nemanja Matic daga Chelsea.

Chelsea da Liverpool suna takara akan sayen dan wasan gaba na kasar Gabon mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, mai suna Emerick Aubameyang.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG