Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jose Mourinho Ya Ce Romelu Lukaku Ba ƙashin Yarwa Ba ne


Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho, ya ce wa magoya bayan Kungiyar ta Manchester united, ya kamata su sani cewar dan wasan gaban kungiyar Romelu Lukaku, ba kashin yarwa bane a wajansa haka ma a wajansu baki daya.

Mourinho, ya bayyana hakane bayan an tashi a wasan da Manchester United, ta doke Tottenham, da ci 1-0 a gasar firimiya lig ta bana a wasannin mako na goma, a ranar Asabar 28/10/2017, inda fadawa magoya bayan kungiyar cewa suna nuna kiyayyarsu ga dan wasan karara a fili.

Magoya bayan kungiyar Manchester united sun nuna cewar dan wasan Lukaku, baya kukari a kungiyar domin baya sha musu kwallaye kamar yadda suka zata zai yi.

Mourinho ya ce ya kamata su sani cewar, ba wai dole sai dan wasa yana cin kwallo ne kawai za'a kirashi dan gaba mai kokari ba, matukar dan wasan yana iya taimakawa a samu nasara a kungiyar, to ya zamo dole a yaba masa.

Romelu Lukaku, ya zo kungiyar ta Manchester united, ne a farkon kakar wasan bana, daga kungiyar kwallon kafa ta Everton, akan kudi fam miliyan £75, ya kuma samu nasarar zurara kwallaye har guda goma sha daya a cikin wasanni goma da ya buga wa Manchester.

Ko a baya bayannan dan wasan ya taimaka a nasarar da Manchester, ta samu akan kungiyar Tottenham da ci 1-0 inda ya ba Anthony Martail, kwallon da ya ci a mintuna na tamanin da daya. Sai dai dan wasan ya kasa jefa kwallo a wasannin baya da Manchester ta buga.

Wannan ba shine karo na farko da magoya bayan kungiyar ke nuna kiyayya ga dan wasanba, a kwanakin bayama sunyi masa wake wake na nuna wariyar launin fata.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG