Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaruman Bollywood Sun Halarci Bikin Ganesha


A duk shekara a kasar Indiya akan yi bikin Giwa, a bisa al’ada, Salman Khan, daya daga cikin mayan jaruman Bollywood, shima ba’a barshi a baya ba wajan wannan bikin domin ya karbi bakuncin gunkin Allan Giwan.

Arpita Khan, kanwar Salman, a bana ta tubure cewa lalle sai iyalin su sun yi bikin Allan Giwan, inda illahirin su suka taru domin sa bikin yayi armashi, kuma ya kasance abun sha’awa.

Bikin ya samu halartar masu harkar fina finai,na Bollywood,wadanda suka kai ziyara gidan Salman Khan, domin ziyarar gunkin Ganesha, wanda ya kwana ya kuma yini a gidan Salman Khan.

Abun sha’awa shine ganin yadda iyalai a lokacin bikin a cikin anashiwa da farin ciki.

Jarumin da iyalinsa sun tabbatar da ganin cewa babu hayaniya a lokacin bikin ta yadda makwabta da jama’ar, da suka halarcin bukin suka more.

Shakrukh Khan, jarumi kamar Salman Khan, shima ya karbi bakuncin wani gunki mai suna Ganpati wanda shima duk cikin dangin gumakan Allan Giwa ne inda suka taru da iyalansa aka yi bikin kamar yadda suke yi a lokacin bikin Sallar Eid.

Bikin Giwa, bikin ne da fitattun jaruman Bollywood, da masu fada aji ke halarta.

Daga cikin jaruman da suka halarci bikin na bana sun hada da Govinda, Shilpa ShettyKundra da Vivek Oberoi,

Bikin bai bar Katrina Kaif, da Kareena Khan a baya ba dama wasu da dama da suka samu ziyarar Gunkin Ganesha a birnin.

XS
SM
MD
LG