Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamus Ta Lallasa Afirka ta Kudu 4-0


Tawagar 'yan wasan kasar Jamus a gasar cin kofin duniya na mata da ke gudana a Faransa
Tawagar 'yan wasan kasar Jamus a gasar cin kofin duniya na mata da ke gudana a Faransa

Tawagar ‘yan wasan kwallon kafar kasar Jamus ta ci gaba da kasancewa a saman teburin rukuninsu na B, bayan da ta doke takwarorinta na Afirka ta Kudu da ci 4-0 a gasar cin kofin duniya na mata.

Yanzu haka Jamus na da maki 9, Spain na biye da ita da maki 4, sai China ita ma da maki 4, sannan sai Afirka ta Kudu wacce ba ta da maki ko daya.

An jima kadan ne kuma tawagar ‘yan wasan Najeriya ta Super Falcons za ta kara da masu masaukin baki Faransa a ci gaba da karawa da ake yi a gasar cin kofin duniya ta mata.

A wannan rukuni na A, Najeriya dai ta sha kaye a hannun Norway da ci 3-0, sannan ta yi nasara akan Korea ta Kudu inda ta doke ta da ci 2-0.

Ita kuwa Faransa ta yi nasarar dukkan wasanninta biyu, inda ta doke Korea ta Kudun da ci 4-0, sannan ta doke Norway da ci 2-1.

Idan Faransa ta doke Najeriya, za ta samu damar shiga zagaye na gaba - ko da kunnen doki ta yi, muddin Norway ba ta doke Korea ta Kudu ba ta kuma rufe gibin yawan kwallaye.

Sauran wasannin da za a buga a yau, sun hada da:

China vs Spain.

Korea ta Kudu vs Norway.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG