Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jabun Magunguna Sun Fi Mamaye Kasashe Masu Tasowa - Bincike


Kimanin daya cikin takwas na magungunan da ake samarwa, musamman a kasashe masu tasowa na dauke da sinadarai marasa amfani, koma ance ana hadasu da sinadarai masu hadari ga rayuwar bil’adama.

Wani bincike da aka gabatar da ya yi dubi kan kimani sakamako 350 na wasu bincike da suka shafi yadda ake samarwa da amfani da maguguna a wadannan kasashe masu tasowa, ya bayyana da cewa, kimanin kashi 14% cikin 100 na magungunan ba su da inganci da suka kamata ayi amfani da su.

Sau da yawa mutane kan sha wasu magunguna ba tare da duba adadin kwanaki da aka dibarwa maganin ba, binciken ya bayyana da cewa kowane magani akan yi shi tare da adadin tsawon lokacin da sinadaran maganin ya kamata a ce suna aiki.

Shan maganin kai tsaye wanda ba likita ya rubuta ma mutun ba, ko shan shi ba bisa ka’ida ba shi ma yakan haifar da wasu cututuka ga rayuwar dan’adam, a cewra binciken.

Nazarin ya kara jaddada muhimncin kauce ma shan magunguna da ba su dauke da ranakun da aka hada su da na lalacewa.

Haka binciken ya kara jaddada muhimancin shan magani bisa ka’idar da likitoci suka gindaya, domin kuwa hakan yana shafar lafiya mutane da suka fito daga kasashe masu tawo, fiye da na sauran kasashe da suka ci gaba.

Mr. Ozawa, shugaban binciken, ya bayyana cewar sau da yawa magunguna na dauke da sinadarai da suka wuce kima, ko kuma akan hada wasu sinadarai da ba su kamata su shiga cikin wasu nau’ukan magungunan ba.

Binciken ya ayyana cewa, daya cikin biyar na magungunan da ake sha a kasashen Afrika na jabune, a cewar mujallar JAMA Network Open, kana magungunan da ba su da ingancin da suka kamata suna zuwa da dan-karan tsada.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG