Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Sana'a Domin Na Zama Abun Koyi Ga Mata Masu Tasowa


A cikin shirin DandalinVOA na masu kananan sana'o'i, mun samu bakunci matashiya mai suna Sa'adiya Aliyu Dagabana, wacce take sana'ar yin kwaliya da dinki, kuma tana da shafin sada zumunta na 'Instagram' Dagabees Beauty inda take tallar irin kwalliyar da take yi.

Baya ga sana'ar kwaliya Sadiya ta tsunduma ga yin takalma na mata da ma na maza, wanda ta kan saro takalman daga birnin Jos.

Sadiya dai ta na mai jan hankalin mata da su tashi domin su zamo masu dogaro da kan su, kuma su kauracewa zama waje daya suna ci ma zaune.

Sannan ta kalubalenci mata, mussaman wadanda suka yi gaba a sana’oi, da ma wasu ayyukan domin su marawa masu tasowa, ta hanyar tallafa musu ko da shawara ce, da kuma tallafawa sana'o'in da suke yi domin su zama manyan gobe su ma su tallafawa masu tasowa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:55 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG