Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Da Burin Bude Kamfanin Sayar Da Kayan Kamshi Da Dandanon Girki - Hussaina


Hussaina Bashir

Hussaina ta ce ta fara sana’ar kayan kamshin na Sizzle and Spice, kimanin shekaru biyar da suka gabata, inda ta ce ta kan yi adadi da dan dama kuma ya danganta da yadda ake bukata.

Ina sana'ar sayar da kayan kamshi na girke-girke kimanin kala 49, wanda nake hada su nake kuma sayar da su, wanda hakan ya sa na zama mai dogaro da kai, kamar yadda Hussaina Bashir Isiyaku ta bayyanawa DandalinVOA.

Hussaina ta ce, ta fara sana’ar kayan kamshin na "Sizzle and Spice," kimanin shekaru biyar da suka wuce, inda ta ce ta kan yi adadi da dan dama kuma ya danganta da yadda ake bukata.

Ta ce tun tana karama take da sha’awar girki, wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa ta tsunduma ga sana’ar kayan kamshi na girki.

Daga baya sai ta fara binciken ire-iren kayan kamshi na girki, inda ta lura cewa sana’a ce mai sauki amma tana neman lokaci sosai da kuma yin bincike.

Sannan ta kuma kara da cewa tana ba da kayan kamshi a sari ga ‘yan kasuwa ko kuma masu sayan daidai.

Duk da cewar dai ba harkar girki ta karanta a jami’a ba hasali ma ta ce ta karanci ilimin kasuwanci ne tsakanin kasa da kasa, wanda hakan ne ma ya bata damar tsunduma cikin sana’ar hannu, kuma ta fara ne da karamin jari.

Yanzu dai ta ce burinta shi ne, ta bude kamfanin sayar da kayan kamshi na girke-girke da za ta dauki ma’aikata da dama.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG