Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina da Tabbaci Akan Yaya Toure


Yaya Toure
Yaya Toure

Koch din Manchester City, Manuel Pellegrini, yace yana da tabbacin cewa Yaya Toure, ba zai bar kungiyar sa ta Manchester City ba duk da kokarin da Inter keyi domin janye shi.

Pellegrini yace dan wasan tsakiya kuma dan asalin kasar Ivory Coast, ya kamsu da kasancewar sa a kungiyar Manchester City, kuma bashi da niyyar barin kungiyar a wannan bazarar.

A can baya wakilin Yaya Toure, ya yi ikirarin cewa an kusa kammala yarjejeniyar komawarsa Inter, amma Pellegrini nada tabbacin babu inda za shi a iya sanisa a yanzu.

Pellegrini ya fadawa ‘yan jaridu a watan daya gabata cewa Yaya Toure, na nan tare da kungiyar Manchester City, domin yana mahawara da ‘yan wasan sa saboda haka ya san tunanin Yaya Toure.

Amma yana mai cewa bashi da tabbacin akan James Milner, ko zai bar kungiyar ko kuma zai kasance dare dasu.

XS
SM
MD
LG