Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar British Council Zata Horas Da Malamai 500,000 A Najeriya


Hukumar tallafawa kasashen renon Ingila wato British Council zata taimakawa Najeriya wajan horas da malaman makaranta 500,000 da gwamnatin tarayya zata iya daukar su aiki domin bunkasa harkokin ilimi a kasar, kamar yadda shugaban hukumar Claran Devane ya bayyana jiya a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban ya kara da cewa horaswar zata mayar da hankali ne musamman wajan koya harkokin sana’a da kuma bunkasa ilimin malaman domin samun ingantaccen amfanin ilimi a kasar.

Devaney a bayyana cewa hukumar na yin iya bakin kokarin ta domin kaiwa lungu - lungu da sako – ako domin cimma burin sun a ganin cewa sun taba duk wani fanni ko sashe da zai bunkasa ilimi a Najeriya.

Daga karshe shugaban ya bayyana cewa hukumar na nan cikin Najeriya kuma zasu duba harkokin ilimi, da zamantakewa, da al’adu da kuma tsaro domin a cewar sa, suga abinda zasu iya koyo domin su koyawa wasu sassa na duniya.

Dan haka ya cancanta hukumar ta taka rawar gani wajan gina harkar ilimi wadda ke cigaba da samun karbuwa a kasar, dan haka hukumar zata dauki nauyin haras da malaman makaranta guda dubu dari biyar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG