Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hrithik Roshan Da Shah Rukh Khan Sunyi Kasuwa A Bollywood


Hrithik Roshan da Shah Rukh Khan
Hrithik Roshan da Shah Rukh Khan

Fim din Hrithik Roshan, mai suna Kaabil da fim mai suna Raees, na Shah Rukh Khan, sune gigagigan fim din da aka dade ana sa idon ganin irin rawar da zasu taka a Bollywood.

Kuma daga duk kan alamu wadannan fina finai sun taka rawar gani a Bollywood, domin jama’a, sun nishadantu sun kuma gamsu da wadannan fina finai, kuma har ila yau fina finan, sun samarda makudan kudade kawo yanzu.

Akwai alamun cewa fina finan zasu ci gaba da taka rawar gani a Bollywood da kuma samarda kudade ga jaruman da suka fitar da fina finan.

A wannan makon fim din Kung Fu Yoga, dama wasu fina finan sun kokarta, ko zasu rawar gani amma fim din Roshan da na Shah Rukh Khan, sun yi masu fintinkau kuma zasu kasance suna jan ragamar fina finai a Bollywood, har zuwa 10, ga watan Fabrairu. Lokacin da ake sa ran cewa fim din Akshay Kumar,Jolly LLB 2, zai fito, fim din da ake ganin cewa zai nemi taka masu birki.

Koda yake kafin wannan lokacin fina finan na Roshan da Shah Rukh Khan, zasu riga sun tara makudan kudade.

Kawo yanzu a nuna fin din Kaabil sau 2200, kuma ya samarda fiye da Naira miliyan 60, inda shi kuwa Shah Rukh Khan nashi fim din ya samarda fiye da Naira miliyan 72, a mako daya abinda ke nuni da cewa fina finan zasu samarda Karin kudade nan gaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG