Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hanyar Magance Annobar Mutuwar Aure


Adam Zanna
Adam Zanna

Wani matashin mawaki Adam Zanna yace ya sauya akallar wakarsa daga ta soyayya da yabo zuwa ga nasiha akan mu’amalar aure tsakanin al’umma duba da irin kalubalen da ma’aurata ke fuskanta ganin yadda aure ke saurin mutuwa.

Ya ce ya koma ga nasiha ne ganin cewar a yanzu mutane sun fi sanya karya da burin a harkokin aure ko wani zaman a aji ko tatsuniya wanda hakan ke haifar da yawa-yawan mutuwar aure.

Yana mai cewar wani auren baya wuce shekara ko watanni a yanzu sai kaji cewa ya mutu wanda hakan rashin ilimin auren ne ke jawo mutuwar aure.

Zanna ya ce banda haka iyaye na taka muhimmiyar rawa musammam ma wajen bada tarbiya ga ‘ya’ya mata da ma mazajen.

Ya kara da cewa da wakarsa ne yake isar da sakonni da wa’azi ga maurata domin kaucewa zaman tankiya a tsakaninsu.

Ya cigaba da cewa da zarar an yawaita wa’azantar ta hanyar waka hakan ne zai fi saurin shiga kunnuwa matasa da ma iyayen domin magance wannan annoba ta sakin aure tsakanin alumma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG