Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon kafa Na Duniya


A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya a Yayinda aka rufe saye da sayarwa na ‘yan wasan kwallon kafa na duniya na kakar wasan bana 2016/2017.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kammala sayen matashin dan wasa mai suna Nabil Touaizi mai shekara goma Sha biyar da haihuwa daga kungiyar Valencia na ‘yan kasa da shekara Sha shida .

Tsohon dan wasan gaba na Arsenal Emmanuel Adebayor ya rattaba hannun a kungiyar Istanbul Basaksehir, Lukas silva ya koma kulob dinsa Cruzeiro bayan ya shafe watanni goma sha takwas a kungiyar Real Madrid a matsayin aro.

Shi kuwa Dembaba ya koma tsohowar kulob dinsa ne Besiktas a matsayin aro daga Kungiyar Shanghai na kasar China.

Yaya Tore yaki amincewa da ya koma Kungiyar Marseilles domin cigaba da taka leda
Alexandre Pato ya koma kungiyar Quanjian daga Valencia akan kudi yuro miliyan Sha takwas

Shi kuwa mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Mourinho yace kaftin din Kungiyar Wayne Rooney, da Ashley Young sunanan a Manchester har zuwa karshe kakan wasan bana.

Dybala na Juventus yaki amincewa da komawa Manchester United, da taka leda yace ya gwammaci ya tafi Real Madrid ko kuma Barcelona.

Arsenal ta amince da sayen mai tsaron baya na Roma Kostas Manolas akan kudi yuro miliyan €55 inda tace zata bada shi aro wa Kungiyar Giallorossi har zuwa karshen kakar wasan bana.

Dan wasan Super Eagles na Najeriya Odion Ighalo ya koma kungiyar Changchun Yatai na kasar China daga Watford akan kudi fam miliyan £20.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:04 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG